Johan Cruyff ya mutu

Image caption Cruyff, ya buga wa Ajax da Barcelona

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na Netherlands, Johan Cruyff, ya mutu sakamakon cutar daji da ya yi fama da ita.

Cruyff, wanda ya buga wa Ajax da Barcelona tamaula ya mutu yana da shekara 68, ya kuma rike kyautar dan wasan da yafi yin fice a Turai sau uku.

Ya lashe kofin zakarun Turai uku a Ajax, ya horar da Barcelona, ya kuma taimakawa Netherlands kai wa wasan karshe na cin kofin duniya a 1974.

Hukumar kwallon kafa ta Netherlands ta ce, "Ba za ta iya bayyana rashin da ta yi ba."