Za a yi sauye-sauye a gasar zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyar Barcelona ce ke rike da kofin zakarun Turai

UEFA na duba yiwuwar watakila ta rage yawan kungiyoyin da suke buga wasannin cikin rukuni a gasar cin kofin zakarun Turai.

An kuma bayar da shawarar a dinga raba rukunnai biyu dauke da kungiyoyi takwas kowanne, maimakon rukunnai takwas dauke da kungiyoyi hudu da ake yi a yanzu.

Mai magana da yawun hukumar kwallon kafa ta Turai ya ce suna tattaunawa da kungiyoyin kwallon kafar nahiyar, amma har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba.

Ba zai yi wu a sauya fasalin gasar cin kofin zakarun Turai da ake yi yanzu ba, karkashin yarjejeniyar da UEFA ta kulla na tallata wasannin a Talabijin da zai kare a shekarar 2017 zuwa ta 2018.