West Ham ta dauki Manuel Lanzini

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption West Ham tana mataki na biyar a kan teburin Premier

West Ham United ta dauki dan Manuel Lanzini, wanda ke buga mata wasa aro daga kungiyar Al Jazira ta hadaddiyar Daular Larabawa.

Lanzini, mai shekara 23, wanda ke taka leda aro ya rattaba hannu kan yarjejeniyar sheakara hudu a Hammers din.

Yarjejeniyar za ta fara aiki ne ranar 1 ga watan Yunin shekarar nan, kuma ba ta dauke da tsawaita zamansa idan ya cika shekarun da ya saka hannu.

Yanzu haka kociyan West Ham, Slaven Bilic, ya tsawaita zaman Dimitri Payet da kuma Cheikhou Kouyate a kungiyar.