Ko Wenger ya kusa bankwana da Arsenal?

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsene bai yi nasara ba ma a kofin zakarun turai, da aka kara tsakanin Arsenal din da Barcelona, inda aka lallasa su da ci 2-0.

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger na fakewa da gasar kofin FA da aka gudanar kakar wasanni biyu da suka gabata, inda suka yi nasarar lashe wasannin da suka kara da Hull City da Aston Villa, wadanda suka dade suna masa fintinkau.

A yanzu dai ba zai iya dogara da tsoffin wasannin su cece shi ba, ga shi bai yi nasarar lashe gasar firimiya ba tun 2003 zuwa 2004, bayan am shammace su da ci 2-1 a wasan na kusa da na karshe (kwata final) da Watford a filin Emirates.

Kociyan mai shekaru 66 ya jima yana jagoran Arsenal, amma idan har kulob din suka karkare kakar wasannin bana hannu shiru, to lokaci ya zo da za a sake duba cigaba da jagorancin Wenger.