Federer ya samu rauni wajen wanka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Roger Federer ya ce, ya yi barka da aka kammala tiyatar raunin da ya samu a gwiwa lafiya, amma ba haka aka so ba.

Roger Federer ya ce ya samu rauni bayan gasar Australian Open din da aka yi a watan Junairu, yayinda ya ke shirin yi wa 'ya'yansa mata biyu wanka.

An yi wa gwarzon mai shekaru 34, wanda ya yi nasarar lashe wasanni 17, tiyata domin gyara jijiyar da ta tsage a gwiwa, inda daga bisani zai dawo a daidai lokacin gasar Miami Open da za a gudanar wannan makon.

Federer ya ce yana murna an kammala tiyatar lafiya, duk da cewar ba haka aka so ba.

"Na so in gama rayuwar ta a wasanni ba tareda ko kwarzane ba" In ji Federer, "Amma kuma sai gashi, abun mamaki da takaici".

Federer na shirin karawa da dan Argentina Juan Martin del Potro a karo na biyu, a gasar Miami Open.