Brazil da Uruguay sun buga wasa 2-2

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ecuador ce ke mataki na daya, Uruguay ta biyu sai Brazil da Argentina da Paraguay

Brazil ta tashi wasa 2-2 da Uruguay a karawar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da suka fafata a ranar Juma'a.

Ana take wasa Brazil ta ci kwallo ta hannun Douglas Costa, kuma a minti na 26 da fara tamaula ta kara ta biyu ta hannun Renato Augusto.

Uruguay din ta farke kwallaye biyun da aka zura mata ta hannun Edison Cabani da Luis Suarez.

Wannan ne karan farko da Suarez ya fara buga wa kasarsa tamaula, bayan da aka dakatar da shi sakamakon cizon da ya yi a gasar cin kofin duniya a Brazil a 2014.

Da wannan sakamakon Uruguay tana mataki na biyu biye da Ecuador wadda ke matsayi na daya a kan teburi a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta Kudancin Amurka.

Brazil da Argentina da Paraguay dukkanninsu na da maki takwas a mataki na uku.