AFCON 2017: Kamaru da Afirka ta Kudu 2-2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamaru ce ke kan gaba a rukuni da maki bakwai, Afirka ta Kudu tana mataki na uku da maki biyu

Kamaru da Afirka ta Kudu sun tashi wasa 2-2 a karawar neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka yi gumurzu a ranar Asabar.

Afirka ta Kudu ce ta fara cin kwallo ta hannun Tokelo Rantie a minti na 17 da fara tamaula, kuma daf da za a tafi hutun rabin lokaci ne Kamaru ta farke kwallon ta hannun Sebastien Bassong.

Nan da nan kuma Afirka ta Kudu ta kara ta biyu a raga ta hannun Clayton Daniels minti biyar da dawo wa daga hutu, kuma Kamaru ta farke minti 17 tsakani ta hannun Nicolas Nkoulou.

Da wannan sakamakon Kamaru tana mataki na daya a kan teburi na 13 da maki bakwai, sai Mauritania ta biyu da maki shida.

Afirka ta Kudu tana mataki na uku a rukunin da maki biyu, inda Gambia ce ta karshe da maki daya kacal