Konta ta kai wasan zagayen gaba a Miami

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Konta ta kai wasan zagaye na uku a gasar Miami Open

Johanna Konta ta kai wasannin zagaye na uku a gasar kwallon tenis ta cin kofin Miami Open.

Konta ta kai wasan zagayen gaba ne bayan da ta doke Danka Kovinic ta Montenegro da ci 6-4 da 6-2, za kuma za ta fuskanci Elena Vesnina ta Rasha.

Shi kuwa Kyle Edmund dan wasan Birtaniya bai kai wasan zagaye na ukun ba, bayan da Novak Djokovic ya casa ci a karawar da suka yi.

Novak Djokovic ya kai wasan zagayen gabaN ne bayan da ya doke Edmund din da ci 6-3 6-3.