Kai Tsaye: Bayanai kan wasanni

Latsa nan domin sabunta shafin

Barkanmu da ziyarta shafin BBC Hausa kai tsaye a kan wasanni. Za mu kawo muku labarai kan wasanni da ke faruwa a Asabar musamman irin wainar da aketoyawa a nahiyar Turai dama duniya.

3:13 Taron magoya bayan Super Eagles da suka kalli karawar da Nigeria ta tashi 1-1 da Masar a filin wasa na Ahmadu Bello da ke jihar Kaduna, a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka. Nigeria za ta ziyarci Masar a karawa ta biyu a ranar Talata.

Hakkin mallakar hoto Getty

3:07 Johanna Konta ta kai wasannin zagaye na uku a gasar kwallon tenis ta cin kofin Miami Open.

Konta ta kai wasan zagayen gaba ne bayan da ta doke Danka Kovinic ta Montenegro da ci 6-4 da 6-2, za kuma za ta fuskanci Elena Vesnina ta Rasha.

2:37 Kano Pillars za ta karbi bakuncin Ifeanyi Ubah a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria wasan mako na tara da za su yi a ranar Lahadi a jihar Kano. Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin

Hakkin mallakar hoto twitter LMCNPFL

Pillars wadda ta buga wasanni bakwai a gasar tana mataki na biyar a kan teburi da 12, ita ma Ifeanyi Ubah wasanni bakwai ta yi, tana kuma da maki 13 a matsayi na hudu.

1:17 Brazil ta tashi wasa 2-2 da Uruguay a karawar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da suka fafata a ranar Juma'a. Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin

Hakkin mallakar hoto AFP

Ana take wasa Brazil ta ci kwallo ta hannun Douglas Costa, kuma a minti na 26 da fara tamaula ta kara ta biyu ta hannun Renato Augusto.

Uruguay din ta farke kwallaye biyun da aka zura mata ta hannun Edison Cabani da Luis Suarez.

12:40 Sakamakon wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya, Arewacin Amurka

 • Jamaica 1 : 1 Costa Rica
 • Haiti 0 : 0 Panama
 • El Salvador 2 : 2 Honduras
 • Guatemala 2 : 0 United States
 • Canada 0 : 3 Mexico

12:35 Wasannin sada Zumunta

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
 • 4:00 Azerbaijan vs Kazakstan
 • 5:00 Russia vs Lithuania
 • 5:30 Poland vs Finland
 • 5:30 Austria vs Albania
 • 6:00 Hungary vs Croatia
 • 8:45 Germany vs England

12:17 Wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka

 • 12:00 Mauritius vs Rwanda
 • 1:30 Seychelles vs Lesotho
 • 2:00 Burundi -- : -- Namibia
 • 3:30 Cameroon vs South Africa
 • 3:30 Jamhuriyar Congo vs Angola
 • 6:00 Cape Verde vs Morocco
 • 7:00 Burkina Faso vs Uganda Round: 3
 • 8:00 Senegal vs Niger