AFCON 2017: Mauritius ta ci Rwanda 1-0

Image caption Gabon ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Afirka a 2017

Mauritius ta samu nasara a kan Rwanda da ci 1-0 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka kara ranar Asabar a Belle Vue.

Mauritius ta ci kwallonta ne ta hannun Francis Rasolofonirina, a fafatawar da suka yi a filin wasa na Anjalay.

Da wannan nasarar da Mauritius ta samu ya sa ta koma mataki na biyu a kan rukuni na takwas da tazarar maki biyu tsakaninta da Ghana wadda ke matsayi ta daya a teburin.

Ita kuwa Seychelles doke Lesotho ta yi da ci 2-0, sai Burundi da ta yi rashin nasara a gida a hannun Namibia da ci 3-1.