Matasa sun taka rawa a tarihin Man U — Giggs

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ryan Giggs ya jinjinawa Van Gaal kan sayen matasan 'yan wasa

<span >Mataimakin kocin Manchester United Ryan Giggs, ya ce kokarin da kungiyar ke yi wajen saka matasa a 'yan wasanta na daga cikin bangare mafi girma a tarihin kulob din.

Giggs ya ce, koci Louis van Gaal ya bai wa matasan 'yan wasa 14 damar shiga tawagar 'yan wasan kungiyar a karo na farko, tun bayan da ya fara jan ragamarta a bazarar 2014.

A wannan lokaci Van Gaal ya kashe kudi kimanin fam miliyan 250 wajen sayo sabbin 'yan wasa.

Mista Giggs ya ce, "Wannan hobbasa za ta zama wani ginshiki na tarihin kungiyar."

Daga cikin matasa 14 da Louis van Gaal ya dauka sun hada da Jesse Lingard da Tyler Blackett da Saidy Janko da Andreas Pereira da Reece James da Paddy McNair da Tom Thorpe da Cameron Borthwick-Jackson da Donald Love da Joe Riley da Marcus Rashford da Regan Poole da Timothy Fosu-Mensah da kuma James Weir.