Masu gasar Premier na nema na -Ibrahimovic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan gaban ya taimakawa wa Ajax lashe kofin Dutch.

Zlatan Ibrahimovic ya ce akwai kungiyoyin gasar Firimiya da dama da ke zawarcinsa.

Dan wasan mai shekaru 34, zai fita daga kwantiraginsa da Paris St-Germain ta Faransa, inda kuma yanzu ake alakanta shi da komawa ko dai Manchester United ko Chelsea ko kuma Arsenal.

Ibrahimovic dan kasar Sweden ya ce,"Akwai wadanda ke zawarcina, amma zamu ga yadda abun zai kasance."

Ibrahimovic dan wasan gaba ya lashe kofuna da dama a kasashen Turai hudu.

Da taimakonsa kungiyar Ajax ta yi nasarar lashe kofin Dutch.