Adebayor ya dawo buga wa Togo tamaula

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Adebayor mai taka leda a kungiyar Crystal Palace

Emmanuel Adebayor zai buga wa Togo wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka da za ta yi da Tunisia ranar Talata.

Rabon da Adebayor ya yi wa kasarsa wasa tun a cikin watan Yunin 2015, lokacin da yaki amsa goron gayyata zuwa Tunisia, a wasan farko da aka doke Togo 1-0.

Tunisia da Togo da Liberia kowannensu na da maki shida a rukuni na daya.

Duk wadda ta jagoranci rukunin ne dai za ta halarci gasar cin kofin nahiyar Afirka da Gabon za ta karbi bakunci a 2017.