Netherlands ta doke Ingila 2-1 a Wembley

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Netherlands bata samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ba

Ingila ta yi rashin nasara a hannun Netherlands da ci 2-1 a wasan sada zumunta da suka kara a Wembley a ranar Talata.

Ingila ce ta fara cin kwallo ta hannun Vardy saura minti hudu a je hutun rabin lokaci, minti biyar da dawowa ne Netherlands ta farke kwallo ta hannun Janssen ta kuma kara ta biyu ta hannun Narsingh.

Ingila ta buga wasan sada zumuntar ne domin shirin tunkarar gasar cin kofin nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci a shekarar nan.

Ga sakamakon wasannin da aka yi:
 • Portugal 2 vs Belgium 1
 • R. of Ireland 2 vs Slovakia 2
 • France 4 vs Russia 2
 • Scotland 1 vs Denmark 0
 • Estonia 0 vs Serbia 1
 • Montenegro 0 vs Belarus 0
 • Georgia 1 vs Kazakhstan 1
 • Macedonia 0 vs Bulgaria 2
 • Greece 2 vs Iceland 3
 • Gibraltar 0 vs Latvia 5
 • Norway 2 vs Finland 0