Super Eagles ta ba wa 'yan Najeriya hakuri

Hakkin mallakar hoto Channels TV Twitter
Image caption Nigeria bata je gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2015 da aka yi ba

Kungiyar wasa ta Super Eagles ta Najeriya ta nemi afuwar 'yan kasar bisa rashin nasarar samun gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Kungiyar ta Super Eagles wadda ta nemi afuwar ta shafinta na Twitter, ta ce 'yan wasan sun yi iya bakin kokarinsu wajen ganin sun shiga gasar amma kuma al'amarin ya ci tura.

A ranar Talata ne dai Masar ta doke Nigeria da ci daya mai ban haushi a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin na nahiyar Afirka.

Masar din ta ci kwallon tane tilo ta hannun Ramadan Sobhy a minti na 17 da dawowa daga hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon da aka tashi Masar tana mataki na daya a kan rukuni na takwas da maki bakwai, sai Nigeria da maki biyu a matsayi na biyu, da kuma Tanzaniya ta uku da maki daya kacal.

Masar wadda ba ta je gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2015 ba, ta samu gurbin shiga fafatawar da za a yi a Gabon a 2017 kenan.

Masar din za ta ziyarci Tanzaniya ranar 2 ga watan Yuni a wasan karshe na cikin rukuni, yayin da Nigeria za ta karbi bakuncin Tanzaniyar ranar 1 ga watan Satumba.