Nigeria VS Egypt: Ya ya wasan zai kaya?

Hakkin mallakar hoto NFF
Image caption 'Yan wasan Super Eagles sun sauka Masar

Da yammacin ranar Talatar nan ne kungiyar wasa ta Super Eagles ta Najeriya za ta fafata da kungiyar Pharoahs da ke Masar, a wasan zagaye na biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka wato AFCON 2017.

A zagaye na farko dai, an tashi 1-1, a wasan da kungiyoyin biyu suka kara, a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna, ranar Juma'a.

Yanzu haka, kasar ta Masar ce jagaba a rukunin na 7 wato group G.

Tuni dai 'yan wasan Super Eagles suka isa birnin Alexandria na Masar domin taka ledar da kungiyar Pharaohs.

Sai dai kuma rahotanni na cewa 'yan wasan na Super Eagles ba su samu damar yin atasaye ba, ranar Litinin sakamakon rashin isa Masar da wuri.

Wannan ne dai wasan da zai ba wa Najeriyar damar cancanta ko akasin hakan wajen buga gasar ta AFCON.