An raba jan kati 13 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto thenff
Image caption An kammala wasannin mako na tara a gasar ta Firimiyar Nigeria

Alkalan gasar Firimiyar Nigeria sun kori 'yan wasa 13 da kuma bayar da katin gargadi guda 293, bayan da aka buga wasannin mako tara a gasar.

Akwa United ce tafi rashin da'a a gasar wadda aka korar mata 'yan wasa uku, sai Abia Warriors da Rivers United wadanda aka bai wa 'yan wasansu bibiyu jan kati.

Kungiyoyin da aka korar musu dan wasa dai-dai a gasar sun hada da El-Kanemi da Giwa FC da Heartland, da MFM da Rangers da kuma Sunshine Stars.

Kungiyar MFM ce tafi karbar katin gargadi wadda aka bai wa 21, sai Ifeanyi Ubah mai 20, yayin da Lobi Stars da Rangers kowannensu aka bai wa 'yan wasansu katin gargadi sau 19.

Akwa Utd da Rivers Utd da kuma Shooting Stars sun karbi katin gargadi sau 16 kowannensu.