Pele ya bukaci Samsung ya biya shi £21m

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pele tsohon dan wasan Brazil na son Samsung ya biya shi diyya

Fitatcen dan wasan kwallon kafa na duniya, Pele ya nemi kamfanin yin laturonik na Samsung da ya biya shi diyyar kudi fam miliyan 21.

Pele ya shigar da kara ne a wata kotu a Chicago inda ya yi zargin cewar kamfanin na Korea ta Kudu ya yi tallar sabon akwatin talabijin dauke da wani dan wasa da ya yi kama da shi.

An kuma saka tallar sabon talabijin din da kamfanin na Samsung ya kirkira a birnin New York na Amurka ba tare da amincewar Pele ba.

An dai yi zargin cewar Samsung ya amince ya yi amfani da tallar ne bayan da suka kasa kulla yarjejeniya a 2013 ta yin amfani da Pele domin tallata kayayyakinsa.