Gasar Premier za ta samu nakasu

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Ficewar Burtaniya daga tarayyar Turai za ta shafi Premier

Daruruwan 'yan wasan kwallon kafa za su rasa damar yin wasa a gasar Premier ta Ingila da sauran yankunan Burtaniya idan kasar ta fice daga kungiyar tarayyyar Turai.

A ranar 23 ga watan Yuni ne 'yan kasar ta Burtaniya za su jefa kuri'ar jin ra'ayi ta ko su ci gaba da zama a kungiyarta EU ko kuma su fice daga cikinta.

An yi kiyasin akwai sama da 'yan wasan kwallon kafa 400 da wannan mataki zai shafa, idan har Burtaniyan ta zabi ficewa daga gamayyar Turan.

Sai dai yayin da wasu masu lura da harkokin wasannin suke ganin lamarin zai iya yin illa ga harkar kwallon kafa a Burtaniyan, wasu kuwa suna ganin hakan zai ba wa matasa 'yan kasar damar fitowa.