Olympics: Kenya na kila-wa-kala

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan tseren Kenya na sahun gaba wajen nasara a gasannin duniya

Zuwan 'yan wasan Kenya gasar Olympics ta Rio, Brazil na zaman kila-wa-kala, bayan da 'yan majalisar dokokin kasar suka tafi hutu ba tare da sanya hannun amincewa da wata muhimmiyar dokar haramta amfani da kwayoyin kara kuzari ba.

Bayan da aka yi ta samun wasu 'yan wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na kasar ne da laifin ta'ammali da kwayoyin kara kuzari, hukumar yaki da amafani da magungunan a wasanni ta duniya, ta sanya wa Kenyan wa'adin zuwa ranar Talata 05-04-16 ta amince da dokar.

To amma sai a ranar Laraba 30-03-16 aka gabatar da dokar gaban majalaisar dokokin kasar, kwana daya kafin 'yan majalisar su tafi hutun kwana goma sha biyu.

Duk da haka shugaban majalisar na iya sake kirawo 'yan majalisar su dawo zama, amma kuma babu alamun zai yi hakan.

Rashin amincewa ko kin bin wannan doka na nufin haramci ga kasar a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya, kuma wannan ya shafi gasar wasannin Olympics.