Cizo: An dakatar da dan wasan Leeds wasa 8

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwallo biyar Souleymane Doukara ya ci a bana

An dakatar da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Leeds United da ke Ingila, daga buga wasanni takwas saboda cizon dan wasa Fulham.

An tuhumi dan wasan ne mai shekara 24 da wannan laifi a wasan da suka yi 1-1 da Fulham a gasar Championship, ranar 23 ga watan Fabrairu, inda ake ganin ya ciji dan wasan baya Fernando Amorebieta.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta kuma ci tarar dan wasan wanda ya musanta aikata laifin, fam dubu biyar, kwatankwacin naira miliyan biyu da 225 000.

Kunyar Leeds ta ce ta ji takaicin hukuncin da kuma tsawon dakatarwar, amma kuma ba za ta kara wani bayani ba sai an bayyana hukuncin a rubuce.

Hukuncin na nufin Doukara ba zai sake buga wa kungiyar wani wasa ba sai na karshe a kakar da ake ciki.