Aston Villa ta dakatar da Agbonlahor

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gabriel Agbonlahor dan wasan gaba ne na Aston Villa

Kungiyar wasa ta Aston Villa ta dakatar da dan wasanta na gaba, Gabriel Agbonlahor, har zuwa lokacin da aka kammala bincike kan zargin shan tabar Shisha.

An dai dauki hoton dan wasan ne a lokacin da yake hutu a Dubai, rike da tabar Shisha.

Yanzu haka, dan wasan mai shekara 29, ba zai buga wasan da kulob din zai buga da Chelsea ba, ranar Asabar.

Aston Villa dai ita ce ta karshe a teburin gasar Premier Ingila.