Akwai barazanar makaman nukiliya- Obama

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaba Obama ya ce, akwai jan aiki gaba idan har ana son tabbatar da makaman nukiliya ba su shiga hannun 'yan ta'adda ba.

Yayin taron duniya akan nukiliya Obama ya ce, an samu ci gaba, amma sanadarin Plutonium da ake amfani da shi wajen haɗa makaman nukiliya yana yaduwa sosai.

Shugaba Obama ya kuma buƙaci kasashe su rika taimakawa juna da bayanan sirri na tsaro domin murƙushe ƙungiyoyi kamar IS.

Sanarwar bayan taron da shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya halarta ta ce, barazanar nukiliya ta na sauya fasali, kuma babban kalubale ne ga tsaron duniya.