Chelsea ta doke Aston Villa da ci 4-0

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Chelsea za ta ziyarci Swansea City a wasan gaba a gasar ta Premier

Aston Villa ta sha kashi a hannun Chelsea da ci 4-0 a gasar Premier da suka kara a Villa Park ranar Asabar.

Ruben Loftus-Cheek ne ya fara ci wa Chelsea kwallon farko, kuma Pato ya kara ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Pedro ya ci wa Chelsea kwallaye biyu, hakan ne ya kuma bai wa kungiyar damar samun maki uku a karawar.

Chelsea za ta ziyarci Swansea a wasan mako na 33, yayin da Aston Villa za ta karbi bakuncin Bournemouth.