Real Madrid ta ci Barcelona 2-1

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cristiano Ronaldo ne ya ci kwallon da ta Real Madrid nasara

Barcelona ta sha kashi a hannun Real Madrid da ci 2-1 a karawarsu ta hamayya da ake wa lakabi da El Classico a gidan Barcelonan Camp Nou.

Pique ne ya fara ci wa Barcelona kwallonta a minti na 56, yayin da Benzema kuma ya farke wa Real Madrid ana minti na 65 da wasan.

A minti na 85 ne Ronaldo ya ci kwallo ta biyu, jin kadan bayan da alkalin wasa ya kori Sergio Ramos bayan ya yi keta kasancewar tun farko ya samu katin gargadi na wata ketar da ya yi.

Duk da rashin nasararta Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a teburin na La liga da maki 76 a wasanni 31, ita kuwa abokiyar hamayyar tata tana matasi na uku da maki 69.

Atletico Madrid wadda ta lallasa Real Betis a karawasu ta Asabar din ta ci gaba da zama a matsayinta na biyu da maki 70.

Las Palmas kuwa ta ci Valencia 2-1, nasarar da ta sa Palmas din take da maki 36 a matsayi na 11 ita kuwa kungiyar Valencita take matsayi na 15 da maki 34.