Miami Open: Djokovic zai kara da Nishikori

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Djokovic da Nishikori za su fafata a wasan karshe a Miami Open

Mai rike da kofin kwallon tennis a gasar Miami Open Novak Djokovic zai kara da Kei Nishikori a wasan karshe a gasar ranar Lahadi.

Djokovic dan kasar Serbia mai matsayi na daya a jerin wadanda suka fi iya tennis, ya kai wasan karshe ne bayan da ya doke Belgian David Goffin da ci 7-6 (7-5) 6-4.

Shi kuwa Nishikori dan kasar Japan ya kai wasan karshe ne, bayan da ya doke Nick Kyrgios da ci 6-3 7-5.

Nishikori yana mataki na shida a jeren 'yan wasan da suka fi iya kwallon tennis a duniya.