Dan Kanawa da Balan Gada sun yi canjaras

Image caption Wannan takawar da suka yi babu kisa a turmi daya da suka yi kacal

Bahagon Dan Kanawa da Bahagon Balan Gada sun tashi wasa babu wanda ya yi kisa a dambatar da suka yi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Bahagon Dan Kanawa ne daga Kudu ya nemi Bahagon Balan Gada daga Arewa su saka zare a tsakaninsu, kuma turmi daya suka taka aka raba su, domin sun sami alheri a karawar.

Tun farko an fara yin wasa ne tsakanin Shagon Hafsat daga Kudu da Abban Na Bacirawa daga Arewa, kuma turmi biyu suka yi alkalin wasa tirabula ya raba su.

Dambe tsakanin Shagon Alhazai Mai Kura daga Arewa da Autan Faya daga kudu turmi biyu suka yi babu wanda ya je kasa a tsakaninsu.

Autan Faya ya kuma sake dambatawa a karo na biyu da Dogon Dan Jamilu daga Arewa, kuma turmi uku suka yi aka raba fafatawar da ba a yi kisa ba.

Wasan karshe kuwa da aka yi Dan Aliyu Shagon Langa-Langa ne daga Arewa ya buge Bokan Dan Sama'ila daga Kudu a turmi na biyu.