Lazio ta kori kociyanta Stefano Pioli

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lazio tana mataki na takwas a kan teburin Serie A

Lazio ta sallami kociyanta Stefano Pioli, bayan da abokiyar hamayyarta Roma ta doke ta da ci 4-1 a gasar Serie A da suka fafata a ranar Lahadi.

Pioli mai shekara 50, ya jagoranci kungiyar kaiwa mataki na uku a gasar ta Serie A da aka yi a bara, amma a yanzu Lazio tana matsayi na takwas da maki 42.

Kungiyar ta nada tsohon dan wasanta, Simone Inzaghi, a matsayin kociyan rikon kwarya zuwa karshen kakar bana.

Lazio ta dauki Pioli aikin mai horar da 'yan wasanta a watan Yunin 2014, bayan da ya jagoranci kungiyoyi da dama ciki har da Bologna da Parma.