Juve na daf da lashe kofin Serie A na bana

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Juventus ta lashe kofin Serie A na Italiya sau 32 jumulla

Juventus na daf da lashe kofin Serie A na bana kuma na biyar a jere, bayan da ta doke Empoli a wasan gasar mako na 31 da suka yi a ranar Asabar.

Juventus din ta samu nasara ne a kan Empolin da ci daya mai ban haushi, kuma Mario Mandzukic ne ya ci mata kwallon kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Da wannan nasarar da Juventus ta samu ya sa tana nan a matsayinta na jagaba a kan teburi da maki 73 daga fafatawa 31 da ta yi a gasar ta Serie A.

Juventus wadda ta lashe kofin karo hudu a jere tun daga kakar wasan 2011/12, tana kuma da guda 32 jumulla, Milan da Inter kowacce ta dauki kofin sau 18.