Za mu lashe kofin Premier — Pochettino

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tottenham tana mataki na biyu a kan teburin Premier

Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino, ya ce har yanzu suna da damar da za su iya lashe kofin Premier, duk da tashi 1- 1 da suka yi da Liverpool.

Tottenham ta tashi wasa kunnen doki da Liverpool a wasan mako na 32 da suka yi a Anfield a ranar Asabar.

Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannu Philippe Coutinho, daga baya Harry Kane ya farkewa Tottenham kwallon, kuma ta 22 da ya ci jumulla a gasar ta bana.

Da wannan sakamakon da suka tashi Tottenham ta ci gaba da zama a mataki na biyu a kan teburi da maki 62, kuma saura wasanni shida suka rage a kammala gasar bana.

Ita kuwa Liverpool tana matsayi na tara da maki 45 a kan teburin gasar, za kuma ta karbi bakuncin Stoke City a wasan mako na 33.

Tottenham, na fatan lashe kofin bana wanda rabon da ta dauki kofin na Premier tun a kakar wasan 1960/61 kuma guda biyu ta lashe jumulla.