Chelsea ta nada Conte sabon kociyanta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Antonio Conte shi ne kociyan tawagar kwallon kafa ta Italia

Chelsea ta nada Antonio Conte, a matsayin sabon kociyanta, wanda zai fara horar da ita a kakar wasannin badi.

Kociyan mai shekara 46, tsohon dan wasan Juventus zai yi aiki a Stamford Bridge kan kwantiragin shekara uku.

Guus Hiddink, wanda ya maye gurbin Jose Mourinho zai ci gaba da jan ragamar kungiyar zuwa karshen kakar wasannin bana.

Conte, wanda ya lashe kofunan Serie A uku a Juventus ya zama mai horar da tamaula na biyar da zai jagoranci Chelsea, bayan Gianluca Vialli da Claudio Ranieri da Carlo Ancelotti da kuma Roberto di Matteo.

Conte shi ne ke jan ragamar tawagar kwallon kafa ta Italiya, kuma shi ne wanda zai kai ta gasar cin kofin Turai da za a yi a Faransa a bana.