Neymar zai bar Barcelona zuwa PSG

Image caption Neymar na taka rawar gani a Barcelona tun lokacin da ya koma kulob din da taka leda

Wakilin Neymar a fagen taka leda ya ce dan wasan zai iya komawa Paris St-Germain da murza leda idan kungiyar ta nuna sha'awar daukar dan kwallon.

Neymar, dan Brazil, ya ci kwallaye 52 a wasannni 86 da ya buga a La Liga, tun komawarsa Barcelona daga Santos a cikin watan Yunin 2013.

Wakilin dan wasan Wagner Ribeiro, ya ce kwantiragin Neymar za ta kare a shekara 2018 da Barcelona.

Neymar yana da yarjejeniyar biyan Barcelona fam miliyan 154 ga duk kungiyar dake da sha'awar dan wasan kafin yarjejeniyarsa ta kare nan da shekara biyu.