Za a ci gaba da gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption za a ci gaba da wasannin mako na 10 a gasar ta Firimiyar Nigeria

Za a ci gaba da karawa a gasar Firimiyar Nigeria wasannin mako na 10 a ranar Laraba.

Cikin wasannin da za a yi Giwa FC za ta karbi bakuncin Kano Pillars, da kuma kai ruwa rana tsakanin Ifenyiubah da Plateau United.

MFM za ta karbi bakuncin Rangers a jihar Legas da kuma fafatawa tsakanin Lobi Stars da Wikki Tourist ta garin Bauchi.

Rangers ce ke mataki na daya a kan teburi da maki 17, sai Ifeanyiubah da maki 16 a matsayi ta biyu, Wikki Tourist da Akwa United da Kano Pillars kowacce tana da maki 15.

Ga wasannin mako na 10 za a yi a gasar ta Firimiya.
  • Shooting Stars vs Stars Ikorodu United
  • Rivers United vs El-Kanemi Warriors
  • Giwa FC vs Kano Pillars
  • IfeanyiUbah vs Plateau United
  • MFM FC vs Rangers International FC
  • Lobi Stars vs Wikki Tourists
  • Akwa United vs Abia Warriors
  • Niger Tornadoes vs Sunshine Stars