Super Falcons za ta ziyarci Senegal

Hakkin mallakar hoto Thenff twitter
Image caption Super Falcons ce ke rike da kofin na nahiyar Afirka

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria, Super Falcons, za ta ziyarci Senegal a ranar Talata domin buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata.

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Senegal za ta fafata ne da ta Nigeria a wasan farko ranar 8 ga watan Afirilu, sannan a yi wasa na biyu a Nigeria ranar 12 ga watan nan a Abuja.

Senegal ta kai matakin buga wasa da Nigeria ne, bayan da ta fitar da Guinea daga wasannin.

Duk tawagar da ta samu nasara a karawa biyu da za su yi, za ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da Kamaru za ta karbi gasa ta 10 da za a yi a bana.

Tuni mai horar da Super Falcons, Florence Omagbemi, ta ce tana da tabbacin za su samu gurbin buga gasar cin kofin na nahiyar Afirka, kuma za su kare kambunsu a Kamarun.