UEFA: Barcelona za ta kara da Atletico Madrid

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Barcelona ce za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a wasan farko na cin kofin zakarun Turai

Barcelona za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a wasan farko na gasar cin kofin zakarun Turai karawar daf da na kusa da karshe a Camp Nou ranar Talata.

Barcelona wadda ta yi wasanni 39 a jere ba a doke ta ba, ta yi rashin nasara a hannun Real Madrid da ci 2-1 a gasar La Liga da suka yi ranar Asabar.

Barca wadda ta lashe kofin zakarun Turai sau biyar, tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 76.

Ita kuwa Atletico Madrid lallasa Real Betis ta yi da ci 5-1 a gasar cin kofin La Liga da suka kara a ranar Asabar.

Atletico tana mataki na biyu a kan teburin na La liga da maki shida tsakaninta da Barcelona.

A dai ranar ta Talata ce Bayern Munich ita kuma za ta karbi bakuncin Benfica a Jamus.