Aston Villa ta fasa hukunta Agbonlahor

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana dai binciken Gabriel ne saboda hotonsa da aka gani yana shan tabar Shisha a Dubai.

Kulob ɗin Aston Villa ya ce ba zai ɗauki ƙarin mataki a kan dan wasansa, Gabriel Agbonlahor ba, bayan bincike kan shan tabar Shisha da ya yi a Dubai.

Kulob ɗin dai ya dakatar da Agbonlahor kuma ya ƙaddamar da binciken cikin gida, bayan samun hoton ɗan wasan riƙe da kwaroron tabar Shisha, a lokacin da yake hutu a Dubai.

Ɗan wasan mai shekara 29, bai buga wasan da Chelsea ta ci ƙungiyar tasa 4-0 ba, ranar Asabar.

Aston Villa ba ta yi nasara ba a wasannin da ta buga guda bakwai ba sannan kuma maki 15 ne suka rage mata ta fita daga gasar Premier.