Har yanzu Barca ba ta karaya ba — Enrique

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi bai ci kwallo ba a wasan da suka yi da Real Madrid. da kuma ya ci to da ita ce kwallonsa ta 500

Kociyan Barcelona, Luis Enrique ya ce ya yi imani da 'yan wasansa za su dauki kofuna, duk kuwa da karya musu lago da Real Madrida ta yi, a wasan da suka tashi 1-2 ranar Asabar.

A ranar Talata ne dai Barca za ta fafata da Atletico Madrid a wasan zagayen farko na wasan dab da na kusa da na ƙArshe na gasar Zakarun Turai.

Enrique ya ce " Saura kaɗan mu manta da rashin nasara a wasa." amma ya ce " 'yan wasansa suna da karfin da za su ci gaba da yadda suke."

Har yanzu dai ana sa ran Barcelona za ta iya daukar kofuna biyar, wannan kakar wasannin.

Tuni kulob ɗin ya ɗauki kofin Uefa Super Cup da na Fifa Club World Cup kuma kungiyar ta yi wa Atletico Madrid tazarar maki 6, a teburin La Liga sannan kuma ta kai ga wasan karshe na Copa del Rey.