An dakatar da Higuain daga buga wasanni

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saura wasanni bakawi suka rage a kammala Serie A

An dakatar da Gonzalo Higuain, na Napoli daga buga wasanni hudu, bayan da ya maida martani cikin fushi, kan jan katin da aka ba shi.

An kori dan wasan ne a karawar da Udinese ta doke Napoli da ci 3-1 a gasar Serie A da suka yi a ranar Lahadi.

Higuin din ya ture alkalin wasa a lokacin da aka ba shi jan katin, har sai da abokin wasansa ya fitar da dan kwallon daga fili.

Shi ma kociyan Napoli, Maurizio Sarri, an dakatar da shi daga buga wasa daya, bisa kalubalantar alkalan wasa da ya yi a lokacin karawar.

Higuain ba zai buga wasan da Napoli za ta yi da Hellas Verona da Inter Milan da Bologna da kuma Roma ba.