Barcelona ta ci Atletico Madrid 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona ce ke mataki na daya a kan teburin La Liga, Atletoco ce matsayi na biyu a kan teburi

Barcelona ta samu nasara a kan Atletico Madrid da ci 2-1 a wasan cin kofin zakarun Turai wasan daf da na kusa da karshe da suka yi ranar Talata a Camp Nou.

Atletico Madrid ce ta fara cin kwallo ta hannun Fernando Torres a minti na 25 da fata tamaula, kuma minti na 35 aka sallami dan wasan daga fili bisa katin gargadi guda biyu da aka ba shi.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Barcelona ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Suarez, sannan ya kara ta biyu saura minti 26 a tashi daga wasan.

Barcelona za ta ziyarci Atletico Madrid a wasa na biyu na gasar ranar Laraba