UEFA: Wolfsburg za ta karbi bakuncin Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Real Madrid suna atasaye

Real Madrid za ta ziyarci Wolfsburg a wasan gasar cin kofin zakarun Turai wasan daf da na kusa da karshe da za su kara ranar Laraba a Jamus.

Real Madrid wadda ta doke Barcelona da ci 2-1 a ranar Asabar, ta dauki kofin zakarun Turai sau 10.

Kuma doke Barcelona da ta yi ne ya kawo karshen wasanni 39 da Barca ta yi ba a samu nasara ba a kanta a wasannin bana.

Ita kuwa Wolfsburg rashin nasara ta yi a hannun Bayer Leverkusen da ci 3-0 a gasar Bundesliga da suka yi gumurzu a ranar Juma'a.

Daya wasan da za a buga a gasar cin kofin zakarun Turan shi ne tsakanin Paris Saint-Germain da Manchester City da za su yi a Faransa.