Za a ci gaba da wasannin Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Za a ci gaba da wasan mako na 10 a gasar Firimiyar Nigeria

Za a ci gaba da wasannin cin kofin Firimiyar Nigeria gasar mako na 10 a ranar Laraba.

Wasu daga cikin karawar da za a yi Giwa FC za ta karbi bakuncin Kano Pillars, Ifeanyi Ubah da Plateau United da kai ruwa rana tsakanin Lobi Stars da Wikki Tourist ta garin Baushi.

MFM za ta kece raini da Rangers a jihar Legas sai Akwa United da Abia United, da kuma wasan da Elkanemi za ta ziyarci Rivers United da barje gumi tsakanin Niger Tornadoes da Sunshine Stars.

Ga jerin wasannin gasar Firimiya da za a buga: