Togo ta nada LeRoy a matsayin kociyanta

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Togo na fatan samun gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka a badi

Hukumar kwallon kafa ta Togo, ta nada Claude LeRoy, a matsayin sabon kociyan tawagar kwallon kafar, domin ya maye gurbin Tom Saintfiet.

Kociyan ya saka hannu kan kwantiragin shekara uku, tare da yarjejeniyar zai kai kasar Togo gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Gabon a 2017.

LeRoy dan kasar Faransa, ya yi aiki a nahiyar Afirka tsawon shekara 30, ya kuma halarci gasar cin kofin nahiyar har sau takwas.

Kociyan ya horar da tawagar kwallon kafar Kamaru da sauran kasashe da suka hada da Senegal da Ghana da Jamhuriyar Congo.