Ana bincike kan kudaden shugaban Fifa

Image caption Infantino shi ne ya maye gurbin Sepp Blatter a Fifa

Jami'an tsaro sun kai samame ofishin hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, domin bincike kan tsohon sakatare janar dinta, Gianni Infantino.

Infantino, wanda shi ne shugaban Fifa na yanzu, an ce yana cikin sunayen da aka fidda na mutanen da suka boye kudade a tsibirin Panama domin kaucewa biyan haraji.

Ana zargin sabon shugaban da cin hanci bayan da ya saka hannu kan yarjejeniyar nuna wasannin kwallo a talabijin a shekarar 2006 tare da wasu 'yan kasuwa biyu.

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta ce za ta bai wa jami'an tsaro duk wasu takardu da suka shafi zargin da ake yi, za kuma ta bayar da hadin kai.

An fallasa labarin yin kwangilar ne bayan da aka samu takardu miliyan 11 na sirrin mutanen da suka ajiye kudade a Panama.

Tun a baya Uefa, ta karyata yin kasuwanci da mutane 14 da hukumar FBI ke bincika kan zargin cin hanci a hukumar ta Fifa.

Infantino ya karyata aikata ba dai-dai ba a hukumar ta kwallon kafar Turai.