Southampton ta yi wa Newcastle 3-0

Image caption Southampton ce ta 7 a teburin Premier

Southampton ta zura kwallaye 3 a ragar Newcastle a wasan da suka yi ranar Asabar.

Dan wasan Southampton, Shane Long ne ya fara jefa kwallon farko sannan Graziano Pelle ya kara ta biyu, ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Shi kuma Victor Wanyama ne ya zura kwallo ta uku.

Yanzu haka Southampton din ce ta 7 a teburin gasar Premeir da maki 50, a inda ita kuma Newcastle take ta 19.