Nigeria: Ana fafatawa a wasan dembe a Sokoto

Image caption Masu son shiga kallon dembe a kan layi

Ranar Juma'a ne aka bude wasannin damben gargajiya da kungiyar dambe ta Nigeria ta shirya, wanda za a yi kwanaki uku ana fafatawa.

Tun farko kungiyar ta umarci shugaban kowacce jiha da ke gabatar da wasan dambe da ya kai ‘yan wasansa da suka yi fice domin barje gumi a gasar a jihar ta Sokoto.

Shugaban kungiyar damben gargajiya ta Nigeria, Ali Zuma ya ce makasudin shirya wannan gasar shi ne dawo da martabar wasan mai dadadden tarihi ga Hausawa da ma duniya baki daya.

Kungiyar ta ware filin wasa na Murtala Square, inda za a dambata da kece raini da kuma yin gumurzu a tsawon kwanaki ukun.

Image caption Wani bangare na masu kallo

Tuni dai aka bude wasannin share fage a ranar ta Juma’a, inda Bahagon Musan Kaduna ya buge Garkuwan Cindo, Shi ma Shagon Samsu Makeri kasha Shagon dan Rabi ya yi.

Daga nan ne aka kammala da wasa tsakanin Shagon Samsu kanin Emi da Dogon Habu na Dutsen Mari, kuma mawakan dambe a fili sune Ali Kwasgara da Yusufu Jango.