Mourinho ba zai je Syria ba - Mendes

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan Disamba ne Chelsea ya kori Jose Mourinho.

Tsohon kociyan Chelsea, Jose Mourinho ya yi watsi da kwantaragin horaswa a kasar Syria, in ji wakilinsa, Jorge Mendes.

Mista Mendes ya ce Mourinho ya faɗawa hukumar ƙwallon ƙafa ta Syria cewa " duk da cewa an karramani da wannan gayyata, amma ba zan iya amsa gayyatar a wannan yanayin ba."

A watan Disamba ne dai kulob ɗin Chelsea ya kori Mourinho a karo na biyu.

Yanzu haka kuma ana alaƙanta Mourinho mai shekara 53, wanda kuma ɗan asalin ƙasar Portugal ne da sansana kulob din Manchester United.