Tsoro ne yake cutar 'yan wasanmu — Benitez

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kociyan Newcastle, Rafael Benitez

Kociyan ƙungiyar Newcastle, Rafael Benitez ya ce tsoron ka da a fidda kulob ɗin daga gasar Premier ta Ingila ne yake hana 'yan wasansa yin katabus.

Maki shida ne kacal ya hana a fitar da ƙungiyar daga gasar.

Benitez ya ce " ....Idan har za mu iya cire tsoro daga ranmu, to za mu iya yin kataɓus. Yanzu ba lokacin sukar juna ba ne."

Wasan da Newcastle ta buga na baya-bayan nan dai shi ne wanda Southampton ta lallasa su da ci 3-1, ranar Asabar.

Yanzu dai wasanni shida ne suka ragewa kulob ɗin da suka haɗa da wasa tsakanin su da Manchester City da Tottenham da kuma Liverpool.