Terry ya ɗauki nauyin jana'izar yaro

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsohon kyaftin din Ingila kuma dan wasan Chelsea, John Terry

Tsohon kyaftin na Ingila, John Terry ya ɗauki nauyin shagalin bikin mutuwar wani yaro mai shekara 8, mai goyon bayan kulob ɗin Chelsea.

Ɗan wasan ya bayar da Fam 1600 ga 'yan uwan mamacin, Tommi Miller wanda suka haɗu da shi, a bara.

Terry ya faɗi cewa ya matuƙar kaɗuwa da samun labarin mutuwar yaron sakamakon cutar dajin jini.

Iyayen yaron sun ce sun yi matuƙar murna da taimakon da Terry ya yi musu.