Har yanzu Kompany yana jin jiki — Pellegrini

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kyaftin din Manchester City, Vincent Kompany

Kociyan Manchester City, Manuel Pellegrini ya ce kyaftin ɗin ƙungiyar, Vincent Kompany ba zai buga wasan da Man City za ta buga da PSG ranar Talata, saboda rashin lafiya.

Manuel Pellegrini ya ce " Bai warke ba ɗari bisa ɗAri."

Kompany, mai shekara 30, bai sake buga wasanni ba, tun bayan raunin da ya samu a ƙafarsa, a lokacin wasansu da Dynamo Kiev, a watan Maris.

Man City dai za ta kara ne da PSG a wasan zagaye na biyu na wasan dab da na kusa da na ƙarshe.

Daman dai sun kara a zagayen farko, a inda suka tashi canjaras wato 2-2.