An kammala wasan damben gargajiya a Sokoto

Image caption Kungiyar wasan damben ta shirya wasannin ne domin maido da martabar al'adun gargajiya
A ranar Lahadi aka rufe wasannin damben gargajiya da kungiyar damben gargajiya ta Nigeria ta shirya a jihar Sokoto, Nigeria.

Kungiyar wasan damben ta shirya wasannin ne domin maido da martabar al'adun gargajiya musamman wasan dambe da ya yi fice a cikin al'ummar Hausawa.

A kuma lokacin ne aka buga wasa tsakanin Ebola da Mai Takwasara 'yan damben da babu kamarsu a tashe a wasan a yanzu haka domin tantance gwani a tsakaninsu.

A ranar Lahadi da yammaci suka dambata tsawon turmi biyu kuma babu wanda ya je kasa a tsakaninsu a fafatawar da suka yi. Ebola dai na bin Mai Takwasara kisa, bayan da ya doke shi a gumurzun da suka yi a Zaria dake jihar Kadunan Nigeria a cikin watan Fabrairun shekaran nan.

Shugaban kungiyar was an damben gargajiya ta Nigeria, Ali Zuma, y ace sun daura aniyar ciyar da was an gaba da nunin haskaka al'adun Hausawa musamman a fagen wasanni a kasa dama duniya a gabaki daya.

Kungiyar ta shiryin yin wasannin da za ta gudanar na gaba a jihar Kano, a gidan damben Mamman Bashar da aka fi sani da suna Dan Liti.